• Labaran yau

  May 30, 2017

  Amurkawa 2 sun mutu wajen taimakon wasu mata Musulmai | isyaku.com

  Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi Allah wadai da kisan wasu Amurkawa su biyu da suka rasa ransu yayin da daya kuma yana jinya a Asibiti sakamakon raunin da ya samu yayin da suke kokarin ceton wasu 'yan mata biyu Musulmai daga takurawa daga wani dan wariyar jinsi a cikin wani jirgin kasa a garin Portland na kasar ta Amurka.

  Matan su biyu sun fuskanci cin zarafi da zagi saboda su Musulmai ne kuma daya tana sanye da Hijabi. Hukumomi sun kama wani wanda aka sha ganinsa a lamurra da suka shafi da'awa na kin jinin baki ko launin fata. Daya daga cikin mamatan tsohon Sojan Amurka ne mai shekara 52.

  Shugaban Trump ya ruwaito a shafinsa na Twitter inda ya kira kisan "abin da baza'a lamunce ba" wannan ya biyo bayan suka da akayi ta yi bayan yayi shiru da farko akan lamarin wanda ya faru a ranar farko na Azumin Ramadana.

  Lamarin dai ya bayar da mamaki a birni da aka sani da hakuri da juna ta fannin addini da fahimda juna duk da banbance-banbance da ke tsakanin mazauna birnin na Portland.An sanya huranni  don karrama mamatan a wajen babban dakin taron birnin bayan an gabatar da addu'oi  da jawabai daga manyan 'yan siyasa da shugabannin Addinai a birnin na Portland. .  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Amurkawa 2 sun mutu wajen taimakon wasu mata Musulmai | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama