Yauri: Rashin bayyanar shugaba da Malamai ya janyo rufe makarantar sakandare a garin Makirin

Gwamnatin jihar Kebbi ta bada umarni a rufe wata makarantar sakandari a garin Makirin da ke karamar hukumar Yauri.

Wamishinan Ilimi na jihar Kebbi shine wanda ya bayar da wannan umarni ya kuma bukaci shuga da malaman makarantar su bayyana a babban sakatariyan ma'aikatan ilimi da ke Birnin kebbi.

Jaridar Daily Trust ta labarta cewa Magawata ya sheda masu cewa tun karfe 8:00 na safe ya je makarantar domin taro na malamai da dalibai da aka saba a bisa al'ada (assembly) amma sia ya tarar cewa babu shugaban makarantar balle malai,sai dalibai kawai.

Kwamishinan ya umarci jami'an da ke sa ido akan harkar koyarwa na shiya-shiya (zonal education inspectors) su buda littafi wanda malamai zasu dinga sa hannu shaidar cewa sun zo aiki a kullum.Ya kuma bayar da umarni cewa duk malamin da bai zo aiki ba har tsawon kwanaki biyar za'a kore shi.Malamin da yayi kwana uku bai zo aiki ba kuma za'a dakatar da shi daga aiki na wucin gadi.

Kwamishina Magawata ya nuna matukar damuwarsa akan wannan lamari,ya kuma ce Gwamnatin jihar Kebbi tana iyakan nata kokari kuma ta bayar da mahimmanci akan harkar ilimi a jihar Kebbi saboda haka rashin yin abin da ya kamata daga bangaren malamai tamkar zagon kasa ne ga kokarin Gwamnatin jihar Kebbi.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
Yauri: Rashin bayyanar shugaba da Malamai ya janyo rufe makarantar sakandare a garin Makirin Yauri: Rashin bayyanar shugaba da Malamai ya janyo rufe makarantar sakandare a garin Makirin Reviewed by on April 11, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.