Wani Kare ya dakile harin bam kan 'yan biki

Wani kare a ya yi mutuwar kasko da wata 'yar kunan bakin wake da tayi kokarin ta rutsa cikin jama'a a wajen da akeyin wani biki.Karen dai ya hana yarinyar isa cikin jama'a kuma a yayin da yake cirka cirka da yarinyar sai bam da take dauke da shi a jikinta ya tashi wanda yayi sanadiyyar mutuwat karen da 'yar kunar bakin waken nan take.

Jaridar premium times ta ruwaito cewa yarinyar tayi kokari ta shiga cikin taron daurin aure ne,a yayin da wannan lamarin ya faru.Rahotanni sun nuna cewa kafin faruwan lamarin awa biyu baya,wasu bama bamai 2 sun tashi a kusa da wajen da ake yin bikin.

Kakakin 'yansandan jihar Borno Victor Isuku ya tabbatar da faruwar lamarin,Victor yace lamarin ya faru ne da karfe 7:30 na safe a unguwar Belbelo da ke cikin karamar hukumar Jere a jihar ta Borno.

Karen dai na wani makwabcin gidan da ake yin bikin ne,kuma bai takura kowaba face ita 'yar kunan bakin waken.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

Wani Kare ya dakile harin bam kan 'yan biki Wani Kare ya dakile harin bam kan 'yan biki Reviewed by on April 02, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.