Uwar yara 8 ta mutu bayan ta zubar da juna biyu da saurayin ta yayi mata

Wata mata uwar yara takwas ta mutu a jihar Ogun a yayin da ta zubar da juna biyu da saurayin ta ya yi mata, matar mai suna Sukurat Adedoyin bayanain sun nuna cewa tana da aure ko kafin aukuwar wannan mummunar lamarin.

Jaridar Sunday Vanguard ta wallafa cewa matar 'yar shekara 33 ta sami kanta cikin wannan yanayi ne bayan saurayin ta mai suna Alabi Kamilu ya banka mata ciki kuma ya bukaci dole ta zubar da cikin inda ita mariganyar ta nemi taimakon wata ma'aikaciyar jinya mai suna Abosede Bello wadda ita ta tafiyar da aikin cire cikin kuma aka sami akasi daga bisani.

Jami'in dan sanda mai gudanar da bincike Asake Morowuntonu ya ce Kamilu saurayin mariganya Sukurat shi ne ya tilasta a dole a cire jikin.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Hoto: Globalhealth
Uwar yara 8 ta mutu bayan ta zubar da juna biyu da saurayin ta yayi mata Uwar yara 8 ta mutu bayan ta zubar da juna biyu da saurayin ta yayi mata Reviewed by on April 30, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.