Putin ya gargadi Trump: Amurka zata fuskanci hakikanin yaki idan ta sake kai wa Syria hari

Bisa dukkan alamu shugaban Rasha Vladmir Putin da Donald Trump na kasar Amurka dangantaka yayi tsami kuma ya kai ga tayar da jijiyoyin wuya bayan harin da Amurka ta kai wa  kasar Syria wadda Rasha ke kawance da ita kuma take goya mata baya.

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya gargadi Amurka akan cewa matsawar ta sake kai hari a kan kasar Syria,lallai ta shirya fuskantar hakikanin yaki.

Amurka tayi awon gaban kanta ne inda ta kai hari da makamai masu linzami akan rundunar sojin Kasar Syria a bisa zargin cewa kasar Syria ta kai harin rashin imani da iskan gas mai lahani akan yankin da 'yan tawaye ke rike da shi a kasar Syria.
Putin ya gargadi Trump: Amurka zata fuskanci hakikanin yaki idan ta sake kai wa Syria hari Putin ya gargadi Trump: Amurka zata fuskanci hakikanin yaki idan ta sake kai wa Syria hari Reviewed by Isyaku Garba on April 10, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.