Mutane 20 sun mutu a zanga-zangar Venezuela

Alkaluman mutanen da suka gamu da ajalinsu a wata zanga-zangar adawa da gwamnatin Venezuela sun kai 20 bayan wata sabuwar arangama ta barke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangara a birnin Caracas.
Jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta harba hayaki mai sa kwalla, in da kuma wasu zaune gari banza suka yi ta harba bindiga kan gidajen al’umma kamar yadda kamfanin Dillancin Labarana Faransa na AFP ya rawaito.
Sai dai wasu rahotanni na cewa, mutane 8 sun rasu ne sakamakon fadowar wayar wutar lantarki kan masu zanga-zangar ganin shugaba Nicolas Maduro ya sauka daga kujersa.
'Yan adawa na zargin gwamnati da hayo 'yan daba don kai musu farmaki a yayin zanga-zangar.

@isyakuweb ku biyo mu a Facebook

Mutane 20 sun mutu a zanga-zangar Venezuela ya fara bayyana a RFI


 
Mutane 20 sun mutu a zanga-zangar Venezuela Mutane 20 sun mutu a zanga-zangar Venezuela Reviewed by on April 24, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.