Masarautar Zuru ta ba Gwamna Rochas Okorocha sarautar "MABUDIN ZURU"

Mai Martaba Sarkin Zuru Maj.Gen Muhammadu Sani Sami 2 ya karbi bakoncin wata babbar tawaga daga jihar Imo zuwa Masarautar Zuru karkashin jagorancin Eze Samuel Ogunwa (Eze Imo) wanda shine mai tafiyar da kungiyar sarakunan gargajiya na Najeriya.

Ogunwa yace sun zo Masarautar Zuru ne domin su gode ma Mai Martaba Sarkin Zuru da jama'ar Masarautar Zuru abisa karramawa da suka yi wa Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha a kan mukamin gargajiya da Masarautar ta bashi na MABUDIN ZURU.Ya kara da cewa Gwamna Rochas ya bukaci a sa wata rana domin nadin nashi saboda bai samu zuwa ba a wannan lokaci da yayi daidai da bukukuwan Uhola na Masarautar Zuru saboda wasu dalilai na aiki.

A yayin da yake maida jawabi,Mai Martaba Sarkin Zuru yace Masarautar ta baiwa Rochas mukamin ne ta la'akari da irin kokarin bayar da taimako da yake yi a Arewacin Najeriya musamman ta bangaren harkar ilimi.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb


Masarautar Zuru ta ba Gwamna Rochas Okorocha sarautar "MABUDIN ZURU" Masarautar Zuru ta ba Gwamna Rochas Okorocha sarautar "MABUDIN ZURU" Reviewed by on April 07, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.