Masarautar Zuru: Sarkin Dabai ya rasu

Rahotu da dumi dumi ya tabbar da cewa Allah yayi wa Alh.Isah Sami Sarkin Dabai na Masarautar Zuru a jihar Kebbi rasuwa a wani Asibiti a kasar Indiya.

Wani sako da Mai Martaba Sarkin Zuru ya fitar ya tabbatar da mutuwar basaraken kuma Sarkin na Zuru yace ana shirin tarbar gawar basaraken a kasar Zuru daga kasar Indiya.

An haifin marigayin a 1963 kimanin shekaru 54 da suka gabata ya rasu ya bar Mata daya da yara uku,na miji daya Mata biyu.

Zamu kawo cikakken rahotu da zarar mun kammala hada bayanai game da rasuwar.

Allah ya jikansa ya gafarta masa kuma ya baiwa iyalansa ikon jure wannan rashin.@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
Masarautar Zuru: Sarkin Dabai ya rasu Masarautar Zuru: Sarkin Dabai ya rasu Reviewed by on April 29, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.