Majalisar Dokoki ta jihar Kebbi ta bukaci tsohon Gwamna Sa'idu Dakingari ya bayyana a gabanta

Majalisar dokoki ta jihar Kebbi ta bukaci tsohon Gwamnan jihar Kebbi Saidu Dakingari tare da wasu 'yan kwangila 6 wadanda suka tafiyar da kwagilar gyaran filin saukan jaragen sama na Sir Ahmadu Bello da ke garin Ambursa da su bayyana a  gabanta cikin makonni uku.

Majalisar ta nada wani kwamiti domin ta binciki yadda aka tafiyar da aikin na filin jiragen saman a 2014 kum a ta gabatar da rahotun ta ranar Talata karkashin jagorancin mataimakin kakakin Majalisar dokoki Hon.Muhammed Buhari Aliero wanda ya sami halartar 'yan majalisa 12.

A cikin rahotun ta mai shafi 27 kwamitin ta zargi 'yan kwangilan da yin karin kudin kwangila,kwamitin tace adadin kudin ya kamata ya kasance N8,623,742,038.80 amma sai aka tsawwala kudin zuwa fiye da N10,615,735,704.56.Kamfanonin da binciken ya shafa sun hada da ;CGC Nigeria Limited, Avsatel Communication limited, General Engineering co-ground lighting limited, Strauss corporation limited, High Global Solid resources limited and Wago Global Venture limited.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb




Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN