Mai Martaba Sarkin Zuru ya fara rangadi a Masarautar sa

Mai Martaba Sarkin Zuru Maj. Gen. (Dr.) Muhammadu Sani Sami CON, Mni, LLD, FICEN, Sami Gomo II ya fara rangadin Kasarsa. Sarkin ya fa...Mai Martaba Sarkin Zuru Maj. Gen. (Dr.) Muhammadu Sani Sami CON, Mni, LLD, FICEN, Sami Gomo II ya fara rangadin Kasarsa. Sarkin ya fara ne da Kasar Wasagu a inda yaziyarci Iyayen Kasa biyar dake wannan Masarauta wato Bena, Wasagu, Kanya, Waje da Ribah.
 
A kowace Fada Mai Martaba Sarkin yakan yabawa Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin Senata Atiku Bagudu da kuma ta Tarayya akan irin ayyukan da sukewa Kasa. Sannan yakarbi koken su tareda kira garesu dasu tabbatarda sun sanya ‘ya’yansu Makaranta musamman Mata, ya kara yin kira garesu dasu dawoda tsarin tsaro irin nada inda kowane Basarake ko Mai unguwa zai tabbatar da bakin da ake samu a Kasarsa na kirki ne ko akasin haka tareda kai rahoton batagari a wurin hukuma. 

Koken da Sarakunan wadannan wuraren sukagabatar sun hada da:1. Kira a tallafa wa ilimin mata a Bena ta hanyar gina Makarantar Sakandare ta jeka ka dawo ta Mata a Bena.

2.  Daukar matakin magance matsalolin iyaka tsakanin Bena da Jihar Niger da kuma Ribah da Kasar Dabai.

3.  Gina Banki a garin Ribah.

4.  Gina Dam tsakanin Ribah da Waje.

5. Kara maida Burtullai da mashekarai da kuma mashaya a hannun Fulani don kaucewa fadan Fulani da Manoma.

6.  Kara inganta tsaro a wannan yanki.

7.  Samarwa matasa ayukan yi a Gwamnatin Tarayya.

A jawabinsa na godiya Mai Martaba Sarkin Wasagu Alh. Mukhtar Musa Muhammad Wasagu ya godewa Mai Martaba akan irin kula da yakewa jama’arsa tare da tabbatar masa wannan yanki nasa an samu tsaro da zaman lafiya. Sai abin da ba’arasa ba sannan ya kara gode masa akan irin ayukkan da ake aiwatarwa a wannan yanki.

COMMENTS

VISITOR
Name

AL-AJABI,22,BIRNIN-KEBBI,21,DUNIYA,19,FADAKARWA,22,FASAHA,3,HOTUNA,34,LABARI,351,NISHADI,49,SANARWA,13,SHARHI,8,SIYASA,15,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Mai Martaba Sarkin Zuru ya fara rangadi a Masarautar sa
Mai Martaba Sarkin Zuru ya fara rangadi a Masarautar sa
https://3.bp.blogspot.com/-RriX7eWOPGk/WQEhgYCT0EI/AAAAAAAAEUU/081DCWk3NTAx09x4EqCG_5Xxn6NcsgnmQCLcB/s400/IMG_20170426_101146.jpg
https://3.bp.blogspot.com/-RriX7eWOPGk/WQEhgYCT0EI/AAAAAAAAEUU/081DCWk3NTAx09x4EqCG_5Xxn6NcsgnmQCLcB/s72-c/IMG_20170426_101146.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/04/mai-martaba-sarkin-zuru-ya-fara-rangadi.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/04/mai-martaba-sarkin-zuru-ya-fara-rangadi.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All WASU KARIN LABARAI LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy