Magu da Daura a Fadar shugaban kasa: yaya zancen tantance Magu ?

A ranar juma'ar da ta gabata ne labarai da hutuna suka bayyana na shugaban hukumar da ke sa ido akan wadanda ke yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati EFCC Ibrahim Magu da shugaban hukumar ayyukan asiri da harkar tsaro na cikin Najeriya DSS Lawal Daura da kuma mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro na kasa NSA Munguno a fadar shugaban kasa ta Aso a Abuja.

Majiyar mu ta labarta mana cewa manyan jami'an gwamnatin sun halara ne a fadar ta shugaban kasa domin tattaunawa akan alkiblar da yaki da cin hanci da rashawa ta fauskanta a Najeriya musamman bayan an gano wasu makudan kudade da hukumar EFCC take bincike akai.

Yanzu haka dai wasu manyan jami'an gwamnatin tarayya suna fuskantar bincike akan makudan kudaden da EFCC ta gano a wani katafaren gida a garin Lagos a 'yan makonnin da suka gabata.Wadanda abin ya shafa sun hada da babban sakataren gwamnati Babachir Lawal da shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya NIA.

@ISYAKUWEB SHAFIN MU NA FACEBOOK
Magu da Daura a Fadar shugaban kasa: yaya zancen tantance Magu ? Magu da Daura a Fadar shugaban kasa: yaya zancen tantance Magu ? Reviewed by on April 23, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.