Kungiyar auren Islama: Shirin aurar da Zawarawa da Budare 100 a jihar Kebbi

Ana shirye shirye akan wani tsari da za'a auratar da mutum 100 a cikin jihar Kebbi wanda wata kungiya da take da'awar cigaban al'ummar jihar Kebbi da ake kira kungiyar auren Islama a jihar Kebbi karkashin jagorancin Mal.Ibrahin Bayawa take shiryawa.

A yayin da ake gudanar da tattaunawa a tsakanin mashahuran mutane da suka halara a wajen,sakataren kungiyar Alh.Abubakar Sambawa ya zana ka'idodin da suka wajaba mabukacin wannan shirin ya tanada kafin ya cika takardar neman samun shiga shirin.Ka'idodin dai suna kunshe a takardar neman shiga shirin watau fom.

Ita dai wannan kungiyar itace irinta ta farko tunda aka sami jihar Kebbi wanda take dauke da wasu karin kudurori na alhairi ga al'umman jihar Kebbi.A cikin shirindai ana sa ran cewa za'a kashe akalla N300,000 akan kowane mutum inda ake son a kashe N200,000 wa Amarya ta hanyar yi mata kayan daki da N150,000 kuma a bata tsabar N50,000 domin ta kara a jallin sana'ar da take yi ko kuma ya zama jalli domin ta yi sana'a.

Shi kuma Ango ana sa ran cewa za'a kashe mashi N100,000 ta hanyar biya mashi sadaki da N50,000 sai kuma a bashi N50,000 domin ya kara a jarin shi.Idan wannan shirin ya samu amincewar Gwamnatin jihar Kebbi,jihar Kebbi zata kasance cikin jerin jihohin arewacin Najeriya kenan da talakawa suka amfana da irin wannan tsarin wanda tuni tsarin ya zama alhairi ga jihohin da suka gabatar da shirin tun farko.

Har ila yau,a cigaba da lalabo hanyoyin da zasu sa akai ga samun nassara akan shirin tsakanin ma'aurata,kungiyar ta tsara yadda zata dinga ilmantar da ma'aurata akan tsari da ka'idan zaman aure,yin taron fadakarwa da karawa juna sani akan harkokin rayuwar zamantakewar aure ta hanyar gayyatan kwararru akan bangarorin da abin ya shafa domin su dinga yin fashin baki,ta gabatar da lakca akan maudu'in shirin.

Kadan daga cikin mambobin kungiyar da suka halarci taron sun hada da Abubakar Labaran Arab da Abubakar Mai Kasset da kuma sauran mutane.An kamala taron tare da amincewa cewa kungiyar zata gayyato sanannun kungiyoyin Mata da ke dauke da manufa irin ta wannan tafiyar domin tantance ka'ida da ingantaccen tsari akan tabbatar da samun nassara a shirin.

Isyaku Garba - Birnin kebbi

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN