Kotu ta umarci 'Yan sanda su biya wata mata Miliyan 20 don cin zarafin ta

Alkalin wata babban kotu a jihar Ekiti Justice Olusegun Ogunyemi ya umarci 'yan sandan jihar Ekiti su biya wata mata mai shekara 51mai suna Mrs Sola Aregbesola naira miliyan 20 a matsayin diyya domin cin zarafinta da kuma keta mutuncin ta ta hanyar tsareta har tsawon awa 72.

Matar tace 'yan sandan a ofishin 'yan sanda na Ilawae a watan Oktoba na bara sun likida mata dukar tsiya,suka daure ta harma suka yi mata rauni lamarinda yasa tace yanzu haka ya haifar mata da rashin gani.Ta kara da cewa rashin jituwa ne tsakaninta da maigidanta akan wani lamarin da ya shafi haraka da wata a waje ya haifar da rigimar da yakai ga 'yan sanda.

Rahotanni sun nuna cewa Alkalin ya kuma umarci 'yan sandan su biya matar wasu karin naira 250,000 zaman kudin magani da ta biya wajen yin jinya.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN