Koriya ta Arewa ta zama bala’i ga kasashen Yamma

Koriya ta Arewa wadda ta zama bala’i ga kasar Amurka saboda irin barazanar da take yi mata ta sake yi wa kasar Australya barazanar kai harin makamin nukliya.
Rahoton da aka samu daga kafafan yada labarai na KCNA na nuna cewa, mai magana da yawun ma’aikatar ministan harkin wajen kasar Koriya ta Arewa ya fitar da wata sanarwa Australiya na goyon bayan kasar Amurka ba tare da sanin abinda ke faruwa ba.
Ministan harkokin wajen Australiya Julie Bishop kuma ya bayyana cewa, “samar da makamin nukliya da Koriya ta Arewa ke yi wata barazana ce ga Australiya” inda ya kara da cewa “idan kasa na irin wannan abu, yana da wuya a ce an ji magana mai dadi daga ministan harkokin wajen kasar. Amma idan ka amince da cewa kai ministan harkokin wajen wata kasa ce, to kamata ne a kula wurin kalaman da zaka yi anfani da shi wurin magana.”
Sanarwar da aka fitar kuma na nuna cewa, kasar Amurka ce ke da alhakin tashin hankalin da ke faruwa a tsibirin Koriya inda aka kara da cewa, “idan Australiya ta cigaba da goyon bayan abinda Amurka ke yi wa kasar Koriya ta Arewa, babu shakka Koriya ta Arewa zata fara kaimata harin makamin nukliya.”
Jiya mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya ziyarci Australiya inda yayi bayanin cewa, “idan ba iya an yi maganin China da Koriya ta Arewa ba, to babu shakka Amurka da kawancenta zata yi hakan.”
Firaministan Australiya Malcolm Turnbul kuma ya bayyana cewa “a kowanne lokaci Koriya ta Arewa tana barazanar zaman lafiyar da ake samarwa” inda ya kara da cewa, kamata ne China ta hanata yin hakan

 Ku biyo mu a shafin mu na Facebook


Koriya ta Arewa ta zama bala’i ga kasashen Yamma ya fara bayyana ne a TRT

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN