Koriya ta Arewa ta yi barazanar yi wa jirgin ruwan Amurka dake gabar tekun kasarta kwaf daya

Koriya ta Arewa ta yi barazanar kifar da jirgin ruwan Amurka dauke da sojoji wanda ke gabar kasarta.
Labaran da kafar yada labarai ta BBC ta fitar na cewa, ofishin yada labarai na jam'iyyar Leba mai mulki a Koriya ta Arewa ya fitar da sanarwa a shafinsa na yanar gizo inda ta ce, gwamnatin kasar ta ba wa sojojin sama umarnin kifar da jirgin ruwan Amurka da jiragen yaki ke tashi da sauka a kansa da zarar ya kawo wani wargi.
Sanarwar ta ce, kifar da jirgin zai zama shaidar nuna karfin sojin Koriya ta Arewa.
Ta kara da cewa, dakarun Koriya ta Arewa a shirye suke da su kifar da jirgin ruwan na Amurka mai aiki da Nukiliya.
Bayan umarnin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayar ne jirgin ruwan na Amurka ya tafi zuwa gabar tekun Koriya ta Arewa.

@isyakuweb ku biyo mu a shafin mu na Facebook

 Koriya ta Arewa ta yi barazanar yi wa jirgin ruwan Amurka dake gabar tekun kasarta kwaf daya ya fara bayyana ne a TRT
 
Koriya ta Arewa ta yi barazanar yi wa jirgin ruwan Amurka dake gabar tekun kasarta kwaf daya Koriya ta Arewa ta yi barazanar yi wa jirgin ruwan Amurka dake gabar tekun kasarta kwaf daya Reviewed by on April 24, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.