• Labaran yau

  Kebbi:Gwamnati ta sayo transfoma 40 akan N150m

  Gwamnatin jihar Kebbi ta sayo transfoma na wutan lantarki guda arba'in domin inganta da kuma samar da wadataccen wutan lantarki a jihar Kebbi.

  Kwamishinan albarkataun ruwa da raya karkara na jihar Kebbi Arch.Bala Sani Kangiwa shi ya shaida wa manema labarai haka jiya a Gidan Gwamnati.

  Kwamishinan ya kara da cewa Gwamnan jihar Kebbi ya amince a sayo transfoma guda 40 akan kudi Naira Miliyan 150 kuma ya bayar da umarni cewa a kaisu domin a sanya su a wajajen da ya kamata a fadin jihar Kebbi.

  Bayanai sun nuna cewa transfoman sun kunshi sunfurin 500KVA guda 28 da kuma 300KVA guda 7 kuma saboda dalilai na ko ta kwana an girka 300KVA guda 5 a Asibitin Hajiya Turai a garin Zauro/Ambursa,Sakatariyar Haliru Abdu da kuma garin Jega.


  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi:Gwamnati ta sayo transfoma 40 akan N150m Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama