Kebbi: Manoma 78,500 sun biya bashin noma

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta karbo kusan Naira biliyan daya daga hannun manoma 78,000 da suka karbi bashi daga babban bankin Najeriya saboda sha'anin noma a jihar ta Kebbi.Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Dabai shine ya shaida wa manema labarai haka a garin Bagudo ranar Laraba da ta gabata.

Tun a baya nedai Gwamnatin jihar Kebbi tayi barazanar cewa zata gurfanar da manoma 11,541 a gaban Kotu idan basu biya kudaden da suka karba rance daga babban bankin ba,wanda hakan ya zaburar da manoman kuma suka biya bashin.

Yombe ya ce Gwamnati bata amfani da bangaren shari'a domin ta muzguna wa kowa face domin a tabbatar da tsarin mutunta yarjejeniya da aka kulla wajen aiwatar da zancen bashin.

@isyakuweb  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook
Kebbi: Manoma 78,500 sun biya bashin noma Kebbi: Manoma 78,500 sun biya bashin noma Reviewed by on April 26, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.