April 26, 2017

Kebbi: Kwararrun Likitoci sun fara duba marasa lafiya kyauta

Gwamnatin jihar Kebbi tare da hadin gwuiwar wasu kwararrun Likitoci daga kasar Amurka guda 60 na Lake Medical Team wanda kungiya ce da ke samar da taimako na harkar Lafiya da hadin gwuiwar kungiyar Likitoci na Najeriya da Ma'aikatar Lafiya na Jihar Kebbi sun fara gudanar da aikin duba marasa lafiya kyauta a cibiyar Lafiya ta jihar Kebbi da ke garin Kalgo da kuma Asibitin Sir Yahaya da ke garin Birnin Kebbi farawa daga ranar 23/6/2017.

Gwamnati ta samar da sabuwar cibiyar Lafiya na jihar Kebbi  KMC a garin Kalgo kilomita 13 daga babban birnin jihar Kebbi domin samar ma al'umma ingantacce da wadataccen kiwon lafiya a cikin jihar wanda ake kyautata zaton zai fara aiki a bana.

Tawagar Likitocin ta kunshi masana na musamman akan Fida da cutuka kamar ciwon makogoro,kunne,ciwon daji,cutar hanji da sauransu.


@ISYAKUWEB      KU BIYO MU A SHAFIN MU NA FACEBOOK

 Hoto: Sophoto Abba Haruna


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: Kebbi: Kwararrun Likitoci sun fara duba marasa lafiya kyauta Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama