Katon Maciji ya hadiye wani mutum


Wani katon maciji Mesa ya hadiye wani manomi dan shekara 25 a tsibirin kauyen Sulawesi ta kudu na kasar Indonesia.Rahotanni sun nuna cewa macijin mai tsawon mita 7ya hadiye Akbar ne a yayin da yaje gonarsa ta itacen manja wanda ke kusa da gidan sa domin ya debo manja.

Makwabta sun banzama cikin daji ne bayan an lura cewa Akbar bai dawo ba daga wajen diban amfanin gona na manja,a yayin da suka ci karo da macijin da dunkulen wani abu a cikin shi.Bayan kauyawan sun kashe macijin kuma suka tsage cikinshi sai suka ga Akbar ne a cikin macijin amma babu rai.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Katon Maciji ya hadiye wani mutum Katon Maciji ya hadiye wani mutum Reviewed by on April 02, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.