Harin Amurka akan Syria,takalar yaki ne ko taimakawa ta'addanci?



Makonni uku da suka gabata,Duniya ta shaida matakai maras takamammen alkibla da kasar Amurka ta dauka game da rikicin kasar Syria.A watan Maris daya gabata kasar Amurka ta kai hari a unguwannin fararen hula a Raqqa,harin da yayi sanadin lalata wata Makaranta da kuma Masallaci haka kuma harin ya janyo mutuwar mutane da dama kuma fararen hula.Bayan mako daya,Nikkey Haley jakadiyar kasar Amurka a Majalisar dinkin duniya ta ce, kasar Amurka bata da bukatar cire shugaban kasar Syria Bashar Al-assad daga mulki da karfin tuwo.

Mako daya bayan jakadiya Nikkey tayi wannan jawabi, kwatsam sai kasar ta Amurka tayi awon gaban kanta ba tare da albarkacin Majalisar dinkin Duniya ba ta kai hari a wani filin sauka da tashi na jiragen sama wanda jiragen yakin  sojojin Rasha da na Syria ke amfani da shi matuka domin sukai hare-hare akan tsigeru ‘yan tawaye a kasar ta Syria.Wannan matakin a karon farko ya nuna yadda kasar Amurka ke takalan sojojin na kasar Syria domin idan sun mayar da martini a bisa dalili na kare kansu ita kuma kasar ta Amurka sai tayi amfani da wannan dama domin ta tsunduma haikan ta fuskanci kasar Syria da yaki gadan-gadan.

Amurka dai karkashin jagorancin Donald Trump,ta kafa hujja ne akan wasu hotuna da aka wallafa wanda ke nuna wasu yara da mutane a yanayi na tagayyara akan zargin cewa anyi amfani da iskar guba ne  akan mutanen.Bayan mumunar bala’I da mutanen kasar Syria ke fuskanta a sanadin wannan yaki,Trump ya bayyana muguntar sa a fili ,a sakamakon harin da sojojin kasar Amurka suka kai akan sojojin Syria,’yan tawayen Syria sunyi murna da wannan lamarin kuma a yanzu haka suna sake hadewa domin su karfafa bayan a ‘yan makonnin da suka gabata sojojin Syria sun ci galaban su har suka tarwatse.

Wannan yana nuna ma Duniya cewa za’a sami canji kenan a irin rawar da kasar Amurka take takawa a rikicin kasar Syria wanda zata jagoranci wasu kawayenta domin akai yaki akan Gwamnatin Bashir Al-asad da kawayen ta?.Idan ‘yan tawayen kasar Syria suna ganin kamar shugaba Trump zai goyi bayan su kai tsaye domin ya taimaka masu su kawar da Gwamnatin Syria,amsa a nan shine sunyi kuskure,domin Trump ba mutum bane da ke tausayin ‘yan kasar Syria akan dalilin cewa babu abin day a tabuka a shekaru shida na yakin domin ya kawo sauki a cikin lamarin.

Wani dali kuwa shine Trump ba zai so yagan cewa Amurka ta maimata kuskuren da take ta yi ba a wannan yankin na gabas ta tsakiya,kamar yadda Gwamnatin Reagan ta taimaka ma Ayatullah Khomeini a 1979 a juyin juwa halin daya zama sanadin kafa kasar Shi’a mafi karfi a Duniya wanda a yanzu haka ta zama barazana ga kasara Amurka.Haka kuma yadda George Bush  ya jagoranci yaki akan Gwamnatin Iraqi ta Saddam Hussein yakin daya zama sanadin kisan wulakanci ga shugaba Saddam Hussei wanda hakan ya haifar da kungiyoyin ta’addanci kamar su IS wanda ta samo asali daga cikin kasar Iraqi.Haka kuma Amuka da Faransa suka jagoranci kashe shuga Mu’ammar Gaddafi na kasar Libya,wanda hakan ya haifar da kungiyoyin ta’addanci da suka zama barazana ga tsaro a yankin Maghreb.

Gwamanati Trump dai bata da kwarewa akan harakokin kasashen Duniya kuma Gwamnati ce da take tafe da rashin farin jinin ta koma bayan abin da aka sani na tsarin kasar Amurka matukar Amurka ta kai hari to zaka gani cewa anyi haka ne domin jinkai ko kawar da ta’addanci kamar yadda muka gani a shugabancin Reagan,Clinton,Bush da Obama.

Awannan yanayin, dole ne akai zukata nesa musamman kasar Rasha saboda idan Rasha tace ta mayar ma Amurka da kaidin ta,lallai Amuka zata dandana kudarta kuwa.Domin idan Rasha ta kara bayar da taimakon makaman linzami da rokoki masu kakkabe jiragen sama da sunfurin rokoki masu dakile hari daga rokoki kwatan kwacin irin wanda Amurka ta harbo wa kasar Syria,lamarin ba zaiyi kyau ba domin yakin na kasar Syria Allah ne kadai ya san lokacin da zai kare.Mafita na siyasa kadai ne abu mafidacewa da zai kawo karshen yakin kasar Syria.

Sharhi daga Isyaku Garba


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN