Gwamnatin PDP tayi kokari a shekaru 16 - Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce jam’iyyar PDP ta fadi zaben shekara ta 2015, amma ba don gazawar gwamnatin ta ba.

Jonathan ya bayyana haka ne a Abuja, inda ya ce a kowace kasa ana samun haka, amma ba don gazawar jam’iyya mai mulki ba, sai domin kawai ‘yan kasa su na bukatar samun canjin shugabanni.

Tsohon shugaban kasar, ya kuma yi watsi da maganganun da gwamnatin APC ke yi cewa, jam’iyyar PDP ba ta tsinana wa Nijeriya komai a tsawon shukaru 16 da ta yi ta na mulki ba.

Jonathan ya kara da cewa, ba bakon abu ne jam’iyyar siyasa ta fuskanci matsala ba, domin a cewar sa, kowane zabe ya na iya zama darasi ga kowace jam’iyyar siyasa.

A karshe Jonathan ya ce, ya na alfahari da cewa jam’iyyar PDP ta taka gagarumar rawa wajen tafiyar da mulkin Nijeriya yadda ya kamata na tsawon shekaru 16.


Liberty
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Gwamnatin PDP tayi kokari a shekaru 16 - Jonathan Gwamnatin PDP tayi kokari a shekaru 16 - Jonathan Reviewed by on April 08, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.