• Labaran yau

  April 30, 2017

  Gesse phase2 Birnin Kebbi: Walimar sauke Qur'ani na Daliban Darul Ulumil Qur'an

  A safiyar yau ne Makarantar Darul-Ulumil Qur'an da ke unguwan rukunin gidaje na Gesse 2 da ke gari Birnin Kebbi ta yaye Dalibai 40 wanda suka sauke Qur'ani a wata walima da mahunkuntar makarantar suka shirya.

  Amma yara Mata guda 24 da yara Maza 16 ne suka sami bayyana cikin karatun da akayi daga cikin dalibai 40 da suka sauke Qur'ani.

  Cikin shiye shirye da aka gabatar ya hada da wasan kwaikwayo da daliban makarantar suka gabatar,pareti,karatu daga Alqur'ani da kuma karatu daga Hadisi.

  A yayin da yake jawabi a wajen taron Malam Haruna Gwandu ya nuna mahimmancin tarbiyyar yara ga iyayen su da kuma Malamai.

  Manyan baki da suka sami halartar Walimar sun hada da babban bako kuma Grand Khadi Muhktar Alkali na sashen shara'ar Musulunci na jihar Kebbi da Hajiya Hadiza Bande Mai kula da sashen adana litattafai na Makarantar koyon fasaha na jihar Kebbi da ke Dakin gari (State polytechnic).


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gesse phase2 Birnin Kebbi: Walimar sauke Qur'ani na Daliban Darul Ulumil Qur'an Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama