April 11, 2017

FRSC: Kwamanda ya yanke gashin wata jami'a da almakashi

Wasu hotuna sun bayyana wanda ke nuna Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC na jihar Rivers Andrew Kumapayi yana yin amfani da almakashi domin ya yanke gashin kai na wasu jami'an hukumar Mata da suka saba dokokin hukumar wajen barin gashin kansu da kuma kitso irin wanda hukumar bata amince da suba.

A yayin da yake gudanar da binciken tsabta akan jami'an FRSC a garin Port hercourt Andrew Kumapayi ya kuma duba jami'an hukumar wanda ya shafi kumbar hannaye,kaki,takalma,hula da dai sauran abubuwan tsabta.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: FRSC: Kwamanda ya yanke gashin wata jami'a da almakashi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama