EFCC ta damke tsohon Gwamnan jihar Niger Babangida Aliyu

Rahotanni da ke fitowa daga Abuja sun nuna cewa hukumar kama masu yi ma tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Niger Dr.Babangida Aliyu a bisa zargin cin hanci da rashawa da halatta kudaden haram.

Majiyar mu ta labarta mana cewa mai magana da yawun EFCC din Mr.Uwajaren ya tabbatar cewa tsohon Gwamanan yana a hannun hukumar ta EFCC kuma suna yi masa tambayoyi.Mr Uwajaren bai yi bayani ko yaushe ne hukumar zata gabatar da tsohon Gwamnan a gaban Kotu ba.

Dr.Aliyu ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga 2007 zuwa 2015,ya kuma sha kaye a zaben da ya tsaya takara na neman kujeran majalisar Dattawa a 2015.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuwebEFCC ta damke tsohon Gwamnan jihar Niger Babangida Aliyu EFCC ta damke tsohon Gwamnan jihar Niger Babangida Aliyu Reviewed by on April 06, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.