DSS ta dakile yunkurin harin ta'addanci kan ofishin jakadancin Amurka da Ingila a Abuja

Rahotanni da suka fito daga birnin Abuja sun nuna cewa Hukumar tsaro na farin kaya DSS ta fitar da wani sanarwa ta hannun mai magana da yawun Hukuman Tony Opuiyo cewa jami'anta sun nassarar dakile wani hari da wasu 'yan ta'adda da ke da alaka da ISIS da kuma Boko Haram suka shirya kaiwa kan ofishin jakadancin Amurka,Ingila da Ofishin jakadancin wasu kasashen yamma a Abuja.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar a yau,ta nuna cewa hukumar ta kama mutanen ne a jihar Benue,sanarwar ta kara da cewa wadanda aka kama sun kammala shirye shirye domin kaddamar da shirin kafin jami'anta su cafke su.Hukumar ta ce wadanda aka kama sun hada da Isa Jibril, Jibril Jibril, Abu Omale Jibril, Halidu Sule da Amhodu Salifu.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


DSS ta dakile yunkurin harin ta'addanci kan ofishin jakadancin Amurka da Ingila a Abuja DSS ta dakile yunkurin harin ta'addanci kan ofishin jakadancin Amurka da Ingila a Abuja Reviewed by on April 12, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.