Buhari ya kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki a Abuja

Rahotanni daga birnin tarayyar Najeriya Abuja sun nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin farfado da raya tattalin arzikin Najeriya.Shugaba Buhari yace yana son ya farfado da Masana'antu Najeriya domin su zama masu dogaro da kansu domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Taron ya samu halartar Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban jam'iyya mai mulki a kasar, John Odigie-Oyegun da shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki da kuma shugaban majalisar wakilan kasar, Yakubu Dogara.

Shirin da ke dauke da manufofi uku ya hada da farfado da tattalin arzikin kasar, da inganta rayuwar 'yan Najeriya da kuma mayar da tattalin arzikin kasar zakaran gwajin dafi a duniya.

Haka kuma shirin zai bukaci ci gaban tattalin arzikin Najeriya da kashi 2.19 cikin 100 a shekarar 2017, inda ake tsammanin tattalin azikin zai karu da kashi bakwai cikin 100 na ma'aunin kididdigar tattalin arziki a shekarar 2020.A yayin da ake son ganin ragewar hauhawan farashin kayaki da kashi 2.19 cikin 100 a shekarar 2017, inda ake tsammanin tattalin azikin zai karu da kashi bakwai cikin 100 na ma'aunin kididdigar tattalin arziki a shekarar 2020.


@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

Buhari ya kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki a Abuja Buhari ya kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki a Abuja Reviewed by on April 05, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.