Biafra: Kotu ta bayar da belin Nnamdi Kanu

Rahotanni da ke fitowa daga Abuja sun tabbatar cewa wata Kotu a Abuja ta bayar da bilin Nnamdi Kanu shugaban kungiyar al'ummar Inyamirai masu kokarin kafa kasar Biafra.

Gwamnati tana tsare da Kanu ne da wasu mutum uku akan zargin cin amanar kasa,wanda mutanen suka musanta a Kotu.

Mai shari'a Binta Nyako ta ce ta bayar da belin ne kan dalilan rashin lafiyar da yake fama da ita.
Sharuddan belin sune sai Mista Kanu ya gabatar da mutane uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.

Mai shari'ar ta kara da cewa ba a yarda a ganshi a cikin taron jama'ar da suka wuce mutum 10 ba.
Ta kara da cewa "kar ya yi hira da 'yan jarida kuma kar ya shirya kowacce irin zanga-zanga".

@isyakuweb Ku biyo mu a shafin mu na Facebook

Biafra: Kotu ta bayar da belin Nnamdi Kanu Biafra: Kotu ta bayar da belin Nnamdi Kanu Reviewed by on April 25, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.