• Labaran yau

  Barazana: Zan kashe Mutum 200 idan Shugaba Buhari ya mutu

  Wani mutum dan gani kashenin Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Inusa Salisu Biu wanda ake zargin cewa dan sanda ne yayi barazanar cewa shi fa zai kashe mutum 200 idan har shugaba Buhari ya mutu.Wannan kalaman sun bayyana ne a shafin nan na sada zumunta na Facebook wanda ya tsokano kace nace tsakanin al'umman kudancin Najriya da na Arewacin kasar.

  Da manema labarai suka tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar ta kasa CSP Moshood Jimoh ya yi bayani cewa suna sane da wadannan kalamai wanda bai dace da matsayin kowane irin jami'in tsaro ba,ya kara da cewa suna kan bincike domin a tantance ko shi wannan mutum jami'in dan sanda ne ko akasin haka kafin a dauki kowane irin mataki.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Barazana: Zan kashe Mutum 200 idan Shugaba Buhari ya mutu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama