Ana zanga zanga akan dakatar da Ndume a Abuja

A yau Talata daruruwan masu zanga zanga suka yi cincirindo a bakin kafar shiga ginin Majalisar Wakilai ta Najeriya a Abuja dauke da kwalaye da kyallaye da ke dauke da kalami da keyin Allah wadai da shugaban Majalisar Dattawa da sauran 'yan Majalisar da suka dakatar da Sanata Ali Ndume wanda ke wakiltar Barno ta kudu a Majalisar Dattawa.

An sami takun saka ne tsakanin Majalisar da Ndume akan furici da yayi akan wasu Sanataoci da hukumar EFCC ke bincike akan zargin cin hanci da rashawa,lamarin da ya kai ga dakatar da shi Ali Ndume har tsawon wata 6.


@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Ana zanga zanga akan dakatar da Ndume a Abuja Ana zanga zanga akan dakatar da Ndume a Abuja Reviewed by on April 04, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.