An yi addu'o'ia daren jiya na Isra'i da Mi'iraji a fadin duniya

A wasu kasashen duniya an gudanar da addu'o'i tare da raya daren Isra'i da Mi'irji wanda ya yi daidai da 27 ga watan Rajab.
A dukkan yankunan Turkiyya Masallatai sun cika da jama'a.
An yi addu'o'i a daren wanda a cikinsa ne Mala'ika Jibrilu Alaihissalam Ya tafi da Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi wa Wasallam daga Makka zuwa Masallacin Aksa sannan zuwa sama.
Shugaban Hukumar Addinai ta Turkiyya Mehmet Görmez ya raya daren a Masallacin Kocatepe da ke Ankara inda ya karanta surar Isra'i tare da kira ga jama'a da su fahimci surar.
Görmez ya ce, wannan lamari wata Mu'ujiza ce da ke nuna mana girma da daukakarmu kasancewarmu bayin Allah madaukakin Sarki.
A Masallacin Hukumar ta Diyanet da ke Washington babban birnin Amurka ma an gudanar da shirin na musamman saboda wannan dare na Mi'iraji.
A Masallacin wanda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bude Musulmai daga jihohi makotan Washington sun halarci taron.
A kasashen Balkan da dama da suka hada da Bosniya, Makedonya da Sabiya an raya daren tare da gudanar da addu'o'i.

@ISYAKUWEB KU BIYO MU A SHAFIN MU NA FACEBOOK

 An yi addu'o'ia daren jiya na Isra'i da Mi'iraji a fadin duniya ya fara bayyana a TRT.
An yi addu'o'ia daren jiya na Isra'i da Mi'iraji a fadin duniya An yi addu'o'ia daren jiya na Isra'i da Mi'iraji a fadin duniya Reviewed by on April 24, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.