• Labaran yau

  April 04, 2017

  An kashe wani Bafillace da ake zargi da satan yara a jihar Kogi

  Wani bawan Allah dan asalin kabilar Filani da ba'a fadi sunan sa ba ya gamu da ajalinsa a hannun wasu mutane da suka fusata bayan an zarge shi da yunkurin satan wata yarinya.

  Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin Ajaka a cikin karamar hukumar Igalamela Odolu sun yi zargin cewa tun dama can aikin shi wannan Bafillacen ne satan Mutane.

  Satan Mutane domin ayi garkuwa da su saboda akarbi fansar kudi ya zama ruwan dare musamman a tsakiya da kudancin Najeriya,har yanzu kuwa hukumomi sun kasa shawo kan yawan karuwar aikata irin wannan laifin.

  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe wani Bafillace da ake zargi da satan yara a jihar Kogi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama