• Labaran yau

  April 27, 2017

  An kashe mutane 5 a tagwayen harin da aka kai a Maiduguri

  Rahotannin daga gwamnatin Najeriya na nuna cewa mutane 5 ne suka mutu a tagwayen hari da aka kai  a Maiduguri na kasar Najeriya inda 11 kuma suka jikkata.

  Kakakin Hukumar bayar agaji gaggawa ta Najeriya Abdulkadir Ibrahim ya shaidawa dan jaridar Anadolu cewa a ranar Laraban nan an kai harin kunar bakin wake 3 a Maiduguri inda mutane  5 suka mutu tare da jikkata 11.

   A gefe guda kuma mai magana da yawun Wyan sandan yankin Victor Isuku ya bayyana cewa daya daga cikin 'yan harin yayi kokarin shiga sansanin masu neman mafaka suke a kauyen Usmati.
  Ya kaa da cewa, "ya kai harin ne a yayin da mutane suka yi kokarin hana shi shiga yankin."

  A halin yanzu an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin jiyya.
  Ko da yake babu wanda ya dauki alhakin harin amma sai dai 'yan sanda sun dora alhakin kan 'yan Boko Haram. Domin a baya ta kai irin wannan hare-haren.  TRT

  @ISYAKUWEB     https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe mutane 5 a tagwayen harin da aka kai a Maiduguri Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama