April 24, 2017

An kashe masu sayerda miyagun kwayoyi biyu a Mexico

An sanarda cewa an kashe wasu masu sayerda miyagun kwayoyi biyu a jihar Tamaulipas dake iyakar Mexico da Amurka.
Sanarwar da aka fitar a ofishin jami’an tsaron jihar Tamaulipas na nuna cewa, an kashe shugaban masu sayerda miyagun kwayoyin a garin Reynosa Julian Loisa Salinas tare da na garin Ciudad Victoria Zetas, Francisco Pancho ne bayan tashin hankali da ya barke tsakaninsu da ‘yan sanda.
A kowanne lokaci ana yawan tashin hankali a tsakanin masu sayer da miyagun kwayoyi a garin Tamaulipas wanda ke iyakar garin Texas na kasar Amurka.

@isyakuweb ku biyo mu a shafin mu na Facebook

 An kashe masu sayerda miyagun kwayoyi biyu a Mexico ya fara bayyana a TRT
 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
Item Reviewed: An kashe masu sayerda miyagun kwayoyi biyu a Mexico Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama