An kama tsohuwar matar shugaban Boko Haram

Jami'an tsaron rundunar tsaro ta farin kaya a Najeriya sun kama wata tsohuwar matar shugaban wani bangare na Boko Haram, Mamman Nur...

Jami'an tsaron rundunar tsaro ta farin kaya a Najeriya sun kama wata tsohuwar matar shugaban wani bangare na Boko Haram, Mamman Nur, a birnin Maiduguri.

Kwamanadan rundunar jami'an tsaron na jihar Borno, Ibrahim Abdu, ya gabatar da Fatima Kabir yar shekara 15 wadda ya ce ta amsa cewar ita tsohuwar matar Mamman Nur ce.

Rundunar tsaron ta ce jami'anta sun kama Fatima ne tare da wata mai suna Amina Salisu a lokacin da suke watangaririya a tashar mota da ake kira Kano Park a birnin Maiduguri ba tare da alamar akwai inda za su ba.

Ko da jami'an tsaron suka musu tambayoyi sai suka amsa cewar an shigo da su Maiduguri ne da nufin kai hare-haren kunar bakin wake.

Kwamandan rundunar tsaro ta farin kayan ya ce bayan anyi wa Fatima gwaji an gane cewar tana dauke da cikin wata hudu.

Har ila yau Ibrahim Abdu ya ce da zaran rundunar ta gama bincike za ta mika matan ga hukumomin domin yin abin da ya dace.


BBC

@isyakuweb  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook

COMMENTS

VISITOR
Name

AL-AJABI,22,BIRNIN-KEBBI,21,DUNIYA,19,FADAKARWA,22,FASAHA,3,HOTUNA,34,LABARI,351,NISHADI,49,SANARWA,13,SHARHI,8,SIYASA,15,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: An kama tsohuwar matar shugaban Boko Haram
An kama tsohuwar matar shugaban Boko Haram
https://3.bp.blogspot.com/-7UcHz1zUM2U/WPaZMejhFPI/AAAAAAAAEJQ/UJjX9w4E8Y4DnfEnU-xebvDdAO7LsiWLgCLcB/s400/boko1.jpg
https://3.bp.blogspot.com/-7UcHz1zUM2U/WPaZMejhFPI/AAAAAAAAEJQ/UJjX9w4E8Y4DnfEnU-xebvDdAO7LsiWLgCLcB/s72-c/boko1.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/04/an-kama-tsohuwar-matar-shugaban-boko.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/04/an-kama-tsohuwar-matar-shugaban-boko.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All WASU KARIN LABARAI LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy