An gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru a Kotu

An gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru Khalid Al-Barnawi tare da wasu mutum shida a gaban wata babbar Kotu a Abuja a bisa tuhumar sa da ta'addanci,sace mutane da kuma kisan gilla.Ansaru dai wani sashe na kungiyar Boko Haram ce da ta balle daga uwar kungiyar.

Mai shari'a John Tsoho na babbar kotun tarayyar Najeriyar da ke Abuja ya bayar da damar kare masu shaida kamar yadda masu gabatar da kara suka nema.

Lauyoyin gwamnati sun kuma nemi alkalin ya ba wa gwamnati damar tsare wadanda ake tuhumar a wani wuri na musamman sabili da tsaro.

Jami'an tsaro na farin kaya sun wuce da mutanen bayan Kotun ta dage zaman ta zuwa ranar 25 ga watan Afrilu.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

An gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru a Kotu An gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru a Kotu Reviewed by on April 11, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.