An fara allurar rigakafin cutar sankarau a wasu jihohin arewacin Najeriya

Hukumomi a Najeriya musamman na kiwon lafiya sun fara rigakafin ciwon sankarau wadda tayi sanadin rasuwar fiye da mutum 300 a Arewacin Najeriya sanadiyyar barkewar annobar sankarau din a wasu jihohi kamar Zamfara,Sokoto Kebbi da kuma Niger.

Rahotanni sun nuna cewa ma'aikatan zasu mayar da hankali ne kan jihar Zamfara wajen da cutar ta yanke saka,kuma ana sa ran za'a yi wa fiye da mutum 500,000 rigakafin cutar wanda yafi kama yara masu shekara biyar zuwa 14.

Nau'in cutar sankarau da aka sani da "meningitis type C" wanda ba a saba samun aukuwar shi a Najeriya ba ne ya jawo barkewar annobar.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
An fara allurar rigakafin cutar sankarau a wasu jihohin arewacin Najeriya An fara allurar rigakafin cutar sankarau a wasu jihohin arewacin Najeriya Reviewed by on April 05, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.