An dakatar da Gandirebobi 3 daga aiki kan sakin Ngileri

Kwamitin kula da harkokin gidajen yari ta Najeriya ta dakatar da wasu hafsoshin kula da gidan Yari su 3 bayan ta zarge su da hada baki domin a saki tsohon Gwamnan jihar Adamawa Bala James Ngileri wanda kotu ta daure akan samunsa da laifin aikata almundahana a lokacin takaitaccen mulkin da yayi.

Hafsoshin da abin ya shafa sun hada da CP Peter Yeni Tenkwa, da DCP Abubakar Abaka da kuma SP John Bukar.A cikin wata sanarwa, wani daraktan kwamitin Mista Sunday Dan Ogu, ya ce an dakatar da jami'an ne sai an kammala dukkan bincike a kan batun.Kawo yanzu babu tabbas kan abin da zai faru ga Mista Ngelari.

Ana zargin  Hafsoshin da laifin hada baki domin a bada rahotu akan rashin lafiyar Ngileri ba bisa ka'ida ba wanda hakan yayi sanadin sakin daurarren tsohon Gwamnan.Rahotun ya nuna cewa rashin lafiyar Ngileri ya tsananta a yayin da yake daure a gidan yari,kuma Asibitin gidan yarin na Yola ba zai iya bayarda kulawa da ya cancanta ba ga tsohon Gwamnan.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
An dakatar da Gandirebobi 3 daga aiki kan sakin Ngileri An dakatar da Gandirebobi 3 daga aiki kan sakin Ngileri Reviewed by on April 05, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.