Zargin Fyade: Basarake yayi wa 'yar shekara 15 fyade a Katsina

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa Majalisar masarautar Katsina ta dakatar da Bashir Bala Kofar-bai daga mukamin sa na Magatakarda, bisa zargin aikata laifin fyade da ake yi masa.

Tun makonni biyu da suka gabata ne Magatakardan ke fuskantar shari'ar aikata fyade ga wata yarinya 'yar shekara 15 a Katsina.Wata majiya ta labarta cewa yarinyar ta fada cikin wannan ibtil'i ne bayan mahaifinta ya aike ta gidan Magatakardan.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakataren Majalisar masarautar Bello Ifo, ya ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take.


@isyakuweb--Ku biyo mu a facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb
Zargin Fyade: Basarake yayi wa 'yar shekara 15 fyade a Katsina Zargin Fyade: Basarake yayi wa 'yar shekara 15 fyade a Katsina Reviewed by on March 24, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.