Za mu dauki nauyi,ka je Amurka ka wanke kan ka,Matasa a Kebbi sun gaya wa Gwamna Atiku

Jaridar nan da ke wallafa labarai ta yanan gizo ta naij.com a wani labari da ta buga a yau Laraba 2/3/2017 ta yi bayani cewa wata kungiya ...

Jaridar nan da ke wallafa labarai ta yanan gizo ta naij.com a wani labari da ta buga a yau Laraba 2/3/2017 ta yi bayani cewa wata kungiya ta hadakar Matasan Arewacin Najeriya ( Northern Youth coalition) ta bai wa Gwamnan jihar kebbi tayin zata biya masa kudin zuwa kasar Amurka domin ya je ya wanke kansa a bisa zargin cewar Gwamnatin kasar Amurka tana neman sa domin tana zargin yana da hannu a kudade da suka kai dalar Amurka Biliyan biyu da tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin Soja ta Janar Sani Abacha ya wawure kuma ya kai kasar ta Amurka ya boye.

Shafin jaridar ya ce wannan bayanin ya biyo bayan kasida ce da Sani Muhammed ya rubuta inda ya kara bayani akan dalilan da ya sa yana da kyau Gwamna Atiku Bagudu ya je kasar ta Amurka domin ya wanke kan shi daga zargin da ake yi mashi wanda ta hakan zai kare martabar shi,da na iyalin shi da kuma kyakkyawar sunan al'ummar jihar Kebbi.Ya kuma ce wannan shine mafi dacewa marmakin ya dinga neman kariya daga Kotunan Najeriya ta hannun Lauyoyin sa,da Alkalan Kotunan Najeriya,wannan bayanan sun fito ne sakamakon takarda da aka raba wa 'yan Jarida wanda Malam Bandiya Birnin kebbi ya sa hannu.

Sun kuma ce zasu biya ma Gwamnan kudin Otal kuma za su yi mashi rakiya domin ya je Amurka ya kare kanshi,sun kara da cewa babu dan Najeriya da zai ki irin wannan tayin da suka yi wa Gwamna Atiku.A ci gaba da bayanin ,sun nuna cewa zai fi kyau ya kai kanshi domin ya kare kanshi a maimakon a fitar da shi zuwa kasar ta Amurka da karfin tuwo domin ya fuskanci zargin da ake yi masa.

SHARHI

Tuhumar al'mundahana ko wawure kudade da ake zargin marigayi Janar Abacha ya yi ta hanyar samun taimakon wasu mutane da ake zargin su ne suka taimaka wajen wawure kudaden kuma suka tsara masa yadda za a kai kudaden domin a boye su.Abacha dai ya rasu ne 8/6/1998 amma har yau an kasa kama kowa,ko kuma a karbo kudaden da ake zargi.An mayar da lamarin a zaman makamin farfaganda ta siyasa da tsari na batanci ga Arewacin Najerya.

Idan za ku tuna ,Gwamnatin Obasanjo ce ta bankado wannan zancen wawuran dukiyar Najeriya da ake zargin Abach ya yi a lokacin mulkin sa,saboda dalilai na siyasa, watau Arewa ta kashe kan ta, ta hanyar cewa ai shugabannin ta barayi ne.Amma idan Maye ya manta,ai uwar Diya bata manta ba,wai Obasanjo ne ya bankado bincike akan cewa Abacha ya saci kudaden Najeriya.Zan ji dadi idan Malam Bandiya Birnin Kebbi za su taimaka su binciko yadda Jirgin sama cike da miliyoyin kudaden Najeriya ya bata a zamanin mulkin Obasanjo a 1978 kuma har yau ba wani bayani.

Isyaku Garba - Birnin kebbi .
@isyakuweb  Ku biyo mu a FacebookCOMMENTS

VISITOR
Name

AL-AJABI,22,BIRNIN-KEBBI,21,DUNIYA,19,FADAKARWA,22,FASAHA,3,HOTUNA,34,LABARI,351,NISHADI,49,SANARWA,13,SHARHI,8,SIYASA,15,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Za mu dauki nauyi,ka je Amurka ka wanke kan ka,Matasa a Kebbi sun gaya wa Gwamna Atiku
Za mu dauki nauyi,ka je Amurka ka wanke kan ka,Matasa a Kebbi sun gaya wa Gwamna Atiku
https://3.bp.blogspot.com/--IDwYn9V_wc/WLhnEjQEZUI/AAAAAAAADUI/nZFDpVKkNysd5PzXeQVVvNNI6ZaM1CfvwCLcB/s320/atiku1.jpg
https://3.bp.blogspot.com/--IDwYn9V_wc/WLhnEjQEZUI/AAAAAAAADUI/nZFDpVKkNysd5PzXeQVVvNNI6ZaM1CfvwCLcB/s72-c/atiku1.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/03/zamu-dauki-nauyika-je-amurka-ka-wanke.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/03/zamu-dauki-nauyika-je-amurka-ka-wanke.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All WASU KARIN LABARAI LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy