• Labaran yau

  March 21, 2017

  'Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 50 a Zaki biam (Hotuna)

  Akalla mutum 50 ne aka kashe a garin Zaki Biam da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue.Garin Zaki Biam dai yayi iyaka ne da garin Wukari na jihar Taraba.Jaridar daily post ta ruwaito cewa a nashi jawabi,wani shugaban al'umma Chief Udom Wuhe yace fiye da 'yan bindiga 10 ne suka shigo garin ta hanyar Tor tonda zuwa Zaki biam inda suka dinga harbi babu kakkautawa wanda nan take yayi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 50 har da 'yan makaranta da ke dawowa gida.


  Wannan lamarin ya farune kasa da mako daya bayan an zargi Filani makiyaya da kashe fiye da mutane 10 a garin Buruku wanda ya sa Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ba Filani awa 72 da cewa su fice daga yankin.

  Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Benue Moses Yamu ya tabbatar da kashe kashe amma ya ce a halin yanzu ba'a gama tantance adadin yawan wadanda aka kashe ba,ya kara da cewa tuni aka tura karin jami'an 'yan sanda domin a maido da zaman lafiya.


  @isyakuweb - Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 50 a Zaki biam (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama