• Labaran yau

  March 18, 2017

  Wata Motar Tilera ta kure konewa a kan titin Ahmadu Bello a Birnin Kebbi


  Da yammaci yau dinnan wata motar tilera da aka loda mata kaya fiye da kima kuma daga kololuwar lodin aka jera korai ta kuru domin har koran da ke saman motar sun kama da wuta a sakamakon tsawo da lodin yayi fiye da kima kuma hakan yayi sanadin tabo wayoyin wutan lantarki wanda ya haddasa tashin gobara a cikin lodin kayakin da ke kan tileran, lamarin ya faru ne akan tiltin Ahmadu Bello gabas da shagon Kabir Arts a garin Birnin Kebbi.

  Nan take direban tileran yayi namijin kokari ya ja motar wayoyin wutan suka ci gaba da bugawa suna haddasa tarnaki da balbalin wutan lantarki amma a hakan direban ya janye tilerar kuma motar ta rabu da wayoyin wutan.Jama'an da ke wajen sun kai dauki na gaggawa kuma aka kashe wutar kafin motar ta kama wuta gabadaya,daga bisani 'yan kwana kwana sun iso wajen amma anriga an kashe wutar kafin su iso.

  Wani da abin ya faru a gabanshi Malam Sani ya dora laifin aukuwan lamarin ne akan zalama da aka nuna ta hanyar shake motar da lodinda ya wuce kima.Ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da cewa su dinga sa ido akan irin wadannan motocin da ake shakewa da lodi wanda suke tabo wayoyin wutan lantarki kuma ta hakan su jawo barna ga wayoyin ko transfoma saboda bugawa da wayoyin ke yi sanadin taba junansu wanda hakan yakan haifar da daukewar wutan lantarki kuma yakan shafi al'umma da yawa da suke amfani da wautan lantarkin.

  Isyaku Garba @isyakuweb
  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wata Motar Tilera ta kure konewa a kan titin Ahmadu Bello a Birnin Kebbi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama