• Labaran yau

  March 18, 2017

  Wata kungiya tana shirye shiryen gabatar wa Gwamnatin jihar kebbi shirin auratar da zawarawa 200
  Wata kungiya karkashin jagorancin Abubakar Sambawa wanda aka fi sani da suna "soja" tana ta kai kawo domin tsarawa da kuma kokarin ta gamsar da gwamnatin jihar kebbi domin ta aiwatar da shirin auratar da zawarawa da kuma budare 200 a fadin jihar kebbi.


  A zantawar da ISYAKU.COM ta yi da soja ,ya yi bayani akan kokari da sukeyi da kuma matakan da suke daukawa domin su tabbatar da ganin cewar wannan shirin ya sami nassara a jihar Kebbi.Tuni dai wasu jihohi kamar su Kano,Sokoto da Katsina sun aiwatar da wannan shirin na auratar da zawarawa,watakila jihar Kebbi tana shirin shiga sahun wadannan jihohin

  Soja yace, shirin ya tanadi kashe akalla N300,000 akan kowane aure guda daya Miji da Mata inda ake son a kashe wa Mace N200,000 wajen yin kayan daki da sauransu shi kuma na miji za'a kashe akalla N100,000 wajen yi mashi sutarar aure,biya masa Sadaki da sauran su.

  Kalli bidiyo a kasa.

  https://web.facebook.com/isyakuweb
  Isyaku Garba @isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wata kungiya tana shirye shiryen gabatar wa Gwamnatin jihar kebbi shirin auratar da zawarawa 200 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama