• Labaran yau

  March 13, 2017

  Wani Mutum ya makale ya mutu a wajen hada wutan lantarki


  Wani jami'in ma'aikatar samar da wutar lantarki ta (Benin Electricity Distribution Company) BDEC da ake kira Kola ya mutu a sanadin makalewa ta hanyar janyo shi da wutar lantarkin ta yi masa a yayin da yake kokarin hada wayoyin wutar lantarki a wani sabon gida da ke anguwar rukunin gidanjen  Gwamnati da ke Itanla a kan titin Ondo zuwa Akure a jihar Ondo.

  Ganau ba jiyau ba ya kara da cewa an gan babur na marigayin an ajiye shi a karkashin bishiyar mangwaro a kusa da inda abin ya faru.Jim kadan ma'aikatan BDEC sun iso gurin da abin ya faru inda manajan hukumar Chris Enuamaka ya tabbatar da cewa marigayi Kola ya je wannan aikin ne ba da izini ko umarnin hukumar ta BDEC ba.Daga bisani jami'an sun sauko da gawar daga kan itaciyar wuntan lantarkin watau palwaya.

  Isyaku Garba @isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook

  AIKO DA LABARI
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani Mutum ya makale ya mutu a wajen hada wutan lantarki Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama