• Labaran yau

  March 17, 2017

  Wani Mutum da dansa sun mutu a cikin Rijiya

  Wani ibtila'i ya faru a wani kauye da ake kira garin Fulani a Karamar hukumar Wamakko kusa da Sokoto inda wani mutum mai suna Malam Umar da danshi Abubakar suka  rasa ransu a yayin da rijiyar da suke hakawa ya ruftawa Abubakar bayan an gina rijiyar har tsawon mita 9.Ganin haka ne ya sa mahaifin Abubakar shima ya tsunduma cikin rijiyar domin ya ceto dansa Abubakar,amma da yake ajali yayi kira babu wanda ya fito da rai a cikin su.


  Rahotanni sun nuna cewa 'yan kwana kwana sun zo wajen da abun ya faru kuma suka fitar da gawakin guda biyu daga bisani aka yi masu sutura

  @isyakuweb   Ku biyo mu a Facebook https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani Mutum da dansa sun mutu a cikin Rijiya Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama