• Labaran yau

  March 20, 2017

  Wani Alfa ya sayi Yaro dan shekara 3 akan N500,ya kashe yaron don Tsafi

  Wani Malami dan kabilar Yarbawa da aka fi sani da Alpha ya kashe wani yaro mai shekara 3 a unguwan Ijegun da ke acikin garin Lagos,Madam Chinasa mahaifiya ga yaron da aka kashe ta shaidda wa manema labaru cewa dan makwabcin ta wanda ake kira Simon shine ya sace danta mai shekara uku ya kaishi wajen Alfa da basu sanshi ko waye ba.


  Simon mai shekaru 15 ya gayawa 'yan sanda cewa wani Alfa ne ya bukaci cewa ya kawo masa yaro mai shekara 3,shi kuma Simon ya garzaya gida inda ya dauko dan makwabcin su ya kai wa Alfa shi kuma Alfa ya bashi N500.Binciken 'yan sanda ya kaiga kamo Simon kuma An kama Alfa amma ko da aka isa wajen da yaron yake an same shi babu rai.

  Yanzu haka Simon da Alfa suna hannun 'yan sanda masu bincike na SCID da ke Panti a jihar ta Lagos.Kwamishinan 'yan sanda na jihar Lagos Mr.Fatai Owoseni yayi kira akan iyaye su dinga sa ido sosai akan zuwa da komowar yaransu domin kaucewa irin wannan ibtila'i.

  @isyakuweb - Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani Alfa ya sayi Yaro dan shekara 3 akan N500,ya kashe yaron don Tsafi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama