• Labaran yau

  March 22, 2017

  Sojoji Sun kona gidaje 47,sun halaka Filani makiyaya 17 a kudancin Kaduna  A wani labari da jaridar Thisday ta buga ,jaridar ta ruwaito cewa shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ya zargi rundunar Sojin Najeriya da cewa sun kashe 'yayan kungiyar ta har mutum 17 kuma suka kona gidaje fiye da 47 a kudancin Kaduna.


  Shugaban kungiyar na reshen jihar Kaduna Alh.Haruan Usman yace sun gayyato Sojojin ne domin su zo su kwantar da tarzoma da take addabar mazauna wannan yankin amma sai Sojojin suka afka ma 'yayan kungiyarta.

  “Wannan kisa dai ba mazauna garin ne suka yi ba, sojoji ne kuma mun san gwamnati tasan da hakan, saboda haka muna jira mu ga abin da zai biyo bayan wannan mumunar al’amari da cin mutunci da sojoji suka yi mana” inji shugaban.
  Ya kara da cewa, Ya yi magana da ‘Garrison Kwamanda’ domin tabbatar da yasan da faruwan wannan al’amari, amma garrison kwamandan ya ce zai sanar da ‘Kwamandin Ofisa na yankin, amma har izuwa yanzu shiru muke ji.

  @isyakuweb -Ku biyo mu a Facebook
   https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sojoji Sun kona gidaje 47,sun halaka Filani makiyaya 17 a kudancin Kaduna Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama