Sashen Hausa na BBC ya cika shekaru 60 da fara watsa shirye shirye

A yau dinnan 24,Maris,2017 sashen Hausa na BBC ya cika shekara 60 da fara watsa shirye shirye kai tsaye daga London zuwa Kasahen yammacin Africa musamman Najerya.Za'a iya tunawa da BBC a kan irin rahotannin da take watsawa wadanda ba sani ba sabo balle nuna bambanci ko son ra'ayi game da lamuran da take watsa labarai akan su.

Wata majiya ta shaida mana cewa sashen Hausa na BBC shine kan gaba a wajen samun yawan masu ziyartar shafin na BBC musamman da wayar salula bisa  kowane sashe na harsuna da BBC take watsa shirye shiryenta.

Ni kaina ,na dauki kacaukam darussa daga Kwalejin koyon aikin jarida na BBC wanda yana daya daga cikin ilimin da nake amfana da shi wajen gabatar da wannan shafin nawa na ISYAKU.COM.

BBC,musamman sahen Hausa tana taka rawa da bazai misaltu ba wajen ilmantarwa,fadakarwa da nishadantarwa musamman ga malam Bahaushe,ko 'yan arewacin Najeriya masu jin harshen Hausa,haka kuma ya fadada zuwa wasu kasashe na yammacin Africa.

Amadadin ni kaina Isyaku Garba da daukacin ma'aikatana na sashen ISYAKU.COM da ZURUONLINE.COM wadanda ke karkashin SENIORA TECH & MULTIPURPOSE SERVICES NIG.LTD ina yi ma sashen Hausa na BBC kyakkyawar fatar alhairi da samun wadataccen ci gaba cikin Salama.Allah ya ja zamanin BBC Hausa !!!





@isyakuweb--Ku biyo mu a shafin mu na Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN