Mutane 46 ne aka kashe a rikicin Ile-Ife

Kimanin mutane 46 aka kashe kuma akalla mutane 100 suka jikata a mummunar rikicin kabilanci da ya faru a garin Ile-Ife da ke jihar Osun.


Hukumar 'yansandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 46,sabanin bayanin da hukumar ta yi tun farko cewa mutum 20 ne aka kashe a rikicin.

Kusan mutane 100 suka jikkata a rikicin tsakanin Hausa da Yarabawa da ya faru a ranar 8 ga watan Maris a unguwannin Sabo da Lagere.

@isyakuweb -Ku biyo mu a Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb
Mutane 46 ne aka kashe a rikicin Ile-Ife Mutane 46 ne aka kashe a rikicin Ile-Ife Reviewed by on March 21, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.