• Labaran yau

  March 09, 2017

  Ministan albarkatun ruwa ya ziyarci Fadamar Birnin kebbi
  Ministan albarkatun ruwa na Najeriya Engnr.Suleiman Adamu ya ziyarci jihar Kebbi kuma ya zarce zuwa wajen aikin noman rani da ke Fadama a garin Birnin kebbi In da yakai ziyar gani da ido na gyaran  Zauro polder project dake fadamar Birnin kebbi.Ministan tare da tawagar sa sun zagaya cikin Fadamar inda suka gane wa idanun su irin kokari da manoman rani ke yin a noman shinkafa,alkama da  sauran su.wannan wurine da ake noman rani na amfani gona iri iri a karkashin kulawar hukumar raya fadamar rima watau Sokoto Rima River Basin Development Authority Birnin kebbi

  Ministan ya bayyana jin dadin sa akan yadda manoma suka dukufa sosai wajen noman na rani,bayan ya duba aikin da ake yi a Gidan ruwa na fadamar domin inganta samar da wadataccen ruwa ga manoma a Fadamar,Ministan ya shawarci manoma akan su dinga aikin taimako na kai-da kai domin samun ingantaccen sakamako a tafiyar da aikin su na noman rani.

  Duk da yake Ministan ya nuna farin ciki akan abin da ya gane wa idanun sa,amma kwanaki kadan kafin zuwan Ministan ,ISYAKU.COM ta zagaya Fadamar inda muka gan manoma suna amfani da ingin ban ruwa mallakin kansu domin samar da ruwa domin amfanin gona da suka shuka.Bincike ya nuna cewa har zuwa wani lokaci ba a samar masu ruwa daga ingin na ban ruwa da yake a Gidan ruwa da ke cikin Fadamar sakamakon matsala da ake kyautata zaton cewa injin din ya fuskanta.

  A nashi jawabi shugaban Manoma na  Fadama Polder Alh.Shehu Mai Bulo wanda aka fi sani da Alh.Shehu Dan Nagwari ya nuna jin dadin sa a kan ziyarar ta Ministan kuma ya yaba wa Ministan akan kokari da ya ce Ministan ke yi domin inganta harkokin albarkatun ruwa da noman rani a Fadamar.

  Kalli bidiyo a kasa

  Isyaku Garba
  @isyakuweb   KU BIYO MU A FACEBOOK
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ministan albarkatun ruwa ya ziyarci Fadamar Birnin kebbi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama