• Labaran yau

  Manoma 250,000 zasu zama Miloniya a jihar Kebbi zuwa karshen 2017

  Gwamnan babban Bankin Najeriya Mr.Godwin Emefiele ya ce Manoma akalla 250,000 zasu zama miloniya yazuwa karshen shekarar nan a dalilin aikin noma a jihar Kebbi.

  Gwamnan yayi wannan tsokaci ne a yayin kaddadmar da kamfanin shinkafa ta WATCOT a garin Argungu na Jihar Kebbi.Kamfanin dai a bisa harsashe zai iya samar da ton 200,000 a kowane shekara.WATCOT Kamfani ne mai zaman kansa.

  Yakuma kara da cewa kimanin Mutane 88,000 ne suka zama Miloniya a jihar Kebbi sakamakon aikin noma,kenan zuwa karshen 2017 ana harsashen cewa Mutane 250,000 zasu zama Miloniya a sakamakon aikin na noma a jihar Kebbi.

  @isyakuweb--Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Manoma 250,000 zasu zama Miloniya a jihar Kebbi zuwa karshen 2017 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama